Sturridge ba zai buga wa Ingila wasa ba

Daniel Sturridge Hakkin mallakar hoto AFPGetty
Image caption Sturridge ya sha jinya a bana kafin ya dawo buga wa Liverpool kwallo

Watakila dan kwallon Liverpool Daniel Sturridge ba zai buga wa Ingila a karawar da za ta yi da Lithuania ba.

Tawagar kwallon kafar Ingilar za ta fafata da Lithuania ne a wasan neman gurbin shiga gasar kofin Nahiyar Turai na shekarar 2016.

Tuni Likitoci suka duba Sturridge dan wasan Liverpool mai shekaru 25, domin auna girman raunin da ya ji a karawar da suka yi da Manchester United ranar Lahadi.

Ingila za ta iya maye gurbin dan wasan da Harry Kane dan kwallon Tottenham, wanda aka gayyato cikin tawagar kwallon kafar kasar a karon farko a makon jiya.