Real Madrid zai yi karar wasu 'yan kallo

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto gett
Image caption Madrid tana mataki na biyu a teburin L a Liga da maki 64

Kulob din Real Madrid ya ce zai dauki matakin shari'a kan magoya baya da suka kai wa 'yan wasansa hari a Barcelona.

Gidan talabijin na Spaniya ne ya nuna hotunan wasu magoya baya suna kartar jikin motar Gareth Bale da ta Jose Rodriguez, bayan da aka kammala wasan da ya yi da Barcelona.

Madrid ya fitar da sanarwar cewa zai dauki dukkan matakin shari'a da ya dace kan wadan da aka samu da laifi.

Kulob din kuma ya ce ya shaida wasu daga cikin magoya baya da suka aikata laifin, ana kuma ci gaba da bincike.

Real Madrid ya yi rashin nasara a hannun Barcelona da ci 2-1 a wasan hamayya da ake yiwa lakabi da El Clasico a ranar Lahadi a Camp Nou.