An dakatar da Skrtel buga wasanni uku

Skrtel De Gea
Image caption Skrtel ya ce ba da gangan ya taka David De Gea ba

Wani kwamitin bincike mai zaman kansa ya ki amincewa da daukaka karar da Martin Skrtel ya yi kan tuhumar da FA ta yi masa, bisa yi wa De Gea keta da gangan.

Sakamakon haka hukumar kwallon kafar Ingila ta dakatar da dan wasan dan kasar Slovakia mai shekaru 30 buga wasanni uku.

Dan wasan ya musanta cewar yana sane ya taka golan a karawar da Manchester United ta doke Liverpool da ci 2-1 a gasar Premier ranar Lahadi.

Skrtel ba zai buga wa Liverpool wasan Premier da Arsenal da Newcastle da kuma kofin kalubale da za su buga wasan daf da na kusa da karshe da Blackburn.

Har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ba ta ce komai ba dangane da lamarin.