Damben Mayweather da Pacquiao zai fi tsada a duniya

Mayweather  Pacquiao Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan biyu za su dambata ne a ranar 2 ga watan Mayu

Damben da za a fafata a tsakanin Floyd Mayweather da Manny Pacquiao zai kasance dambe mafi tsada da za a kalla a talabijin da a tarihin tashoshin talabijin din da ake biya don kallonsu a Birtaniya.

Tashar talabijin ta Sky Sports Box ce za ta nuna wasan ranar Asabar 2 ga watan Mayu, bayan da aka ba ta hakkin nunawa daga babban filin dambe na MGM da ke Las Vegas a Amurka.

Tashar za ta karbi kudin da ya kai fam 24.95 daga masu sha'awar kallon wasan.

Fam 14.95 aka karba a wajen wadanda suka kalli damben Ricky Hatton da Mayweather a shekarar 2007.

Wannan wasa ne ya fi yawan masu kallo a talabijin kasancewar akwai mutane miliyan daya da dubu dari biyar da ke sha'awar kallonsa.

Tashar ta Sky ta ce wannan ne damben da zai fi kowanne tsada a wasannin damben da ta taba nunawa.

A Amurka, tashoshin talabijin na Showtime da HBO za su caji duk mai sha'awar kallon wasan fam 65.

Ana sa ran za a samu kudin da ya kai fam miliyan 152 daga wannan dambe, wanda aka kwashe shekaru shida ana tattaunawar shirya shi.