FA za ta hukunta Ronaldo domin murnar cin kwallo

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga

Watakila hukumar kwallon kafar Spaniya ta hukunta Cristiano Ronaldo, sakamakon murnar farke kwallon da Barcelona ta ci su ranar Lahadi.

Dan wasan ya yi nuni da hannayensa cewa 'yan kallo su kwantar da hankalinsu, lamarin da FA ta ce hakan zai iya harzuka 'yan kallo.

Shugaban gasar kwallon Spaniya Javier Tebas ya ce za su yi bincike ne domin tabbatar da cewa irin wannan nunin ba zai kawo tarzoma ba a filin wasa.

Ya kara da cewa suna kokarin kaucewa hatsarin da ya faru da magoyin bayan Deportivo La Corunya wanda aka kashe a rikicin da ya barke bayan kammala wasa.

Tebas ya ce ya kamata su hukunta Ronaldo, watakila su ci tarar sa ko kuma su dakatar da shi daga buga wasa.

Barcelona ce ta lashe Real Madrid da ci 2-1 a wasan hamayya da ake yi wa lakabi da El Classico ranar Lahadi a Anfield.