Ingila za ta sabunta kwantiragin Hodgson

Roy Hodgson Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hodgson ya karbi aikin horar da Ingila a shekarar 2012

Shugaban hukumar kwallon kafar Ingila Grek Dyke, na shirin tattaunawa da kocin tawagar kwallon kafar Ingila Roy Hodgson kan tsawaita kwantiraginsa a badi.

Hodgson mai shekaru 67, wanda ya maye gurbin Fabio Capello a watan Mayun 2012, ya kasa kai Ingila wasan zagaye na biyu a gasar kofin duniya da aka yi a Brazil.

Sai dai kuma Ingila ce ke kan gaba a rukunin da take buga wasannin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai, bayan da ta lashe wasanni hudu da ta yi.

Kwantiragin Hodgson zai kare da Ingila bayan kammala gasar cin kofin Nahiyar Turai a shekarar 2016, sai dai Dyke ya ce za su tattauna a badi domin tsawaita kwantiragin kociyan.

Ranar Juma'a ne Ingila za ta kara da Lithuania a Wembley a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai, wanda take rukuni daya da Switzerland da San Marino da Estonia da kuma Slovenia.