FA ta dakatar da Les Ferdinad wasa daya

Les Ferdinand
Image caption Ferdinand ya fara aikin Daraktan wasanni a QPR a watan Oktoba

Hukumar kwallon kafar Ingila, ta hukunta daraktan wasanni na kulob din QPR, Les Ferdinad saboda samunsa da rashin da'a.

Haka kuma FA ta ci tarar Ferdinand mai shekaru 48 fam 12,000, ta kuma ce ba zai ziyarci dakin sauya kayan 'yan wasa da hanyar da suke bi su shiga fili ba.

An samu Ferdinand da laifin ne a karawar da Tottenham ta doke QPR da ci 2-1 a gasar Premier, a inda ya fadawa alkalin wasa bakaken maganganu.

Hukumar ta ce hukuncin da ta yanke wa Ferdinad wanda ya karbi aiki da QPR a watan Oktoba ya fara aiki nan take.

QPR tana mataki na 19 a kan teburin Premier da maki 22.