Barca za ta hadu da Athletic Bilbao a Nou Camp

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Filin wasan Barcelona, watau Nou Camp.

Za a yi wasan karshe tsakanin Athletic Bilbao da Barcelona a filin wasan Barcelona watau, Nou Camp a ranar a ranar 30 ga watan Mayu.

Mafi yawancin lokuta, a kan yi wasan karshe na Copa Del Rey, a filin wasan da ba na kulob kulob din da ke fafatawa ba.

Tun 2002 lokacin da Deportivo La Coruna ta doke Real Madrid a gidanta, rabon wani kulub da ke buga wasan karshe ya murza leda a filin gidansa.

Filin kwallon Sevilla, watau Vicente Calderon da na Valencia, Mestalla, a baya su ke gaba gaba domin daukar bakuncin wasan karshen, amma sai aka fitar da su aka bai wa filin kwallon Barcelona wacce ta fi ficce a duniya.

Idan Barcelona ta yi sa'ar samun nasara, za ta lashe kofin Copa del Rey na 27 ke nan, Bilbao kuma ta lashe sau 23.