'Yan kallon Premier za su yi zanga-zanga

Premier League Fans Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana korafin cewa tikitin kallon gasar Premier ya yi tsada

Masu kallon Premier za su yi zanga zanga kan tsadar tikitin kallon wasannin a lokacin da manyan jami'an gasar za su gudanar da babban taronsu.

Babban jami'in gasar Richard Scudamore, zai gabatar da wasika ga masu ruwa da tsaki a gasar a lokacin da za a gudanar da taron a Otal din dake tsakiyar Landan.

Haka kuma Scudamore, zai gabatar da takarda a madadin 'yan kallo da kuma rukunan magoya bayan manyan kungiyoyin gasar Premier su 20.

Wasikar ta bukaci a sabunta bukatar rage farashin kallon wasa, idan kungiya za ta yi wasa a waje ga magoya baya a kakar wasa zuwa fan 20.

Haka kuma a cikin wasikar 'yan kallo sun yi kira da cewa ko wacce kungiya ta tanadi fam miliyan daya a kakar wasa domin saukaka wa magoya baya kallon wasan da bana gida ba.

Sannan kuma a yi tanadi na musamman ta yadda za a dinga tuntubar magoya bayan kungiyoyin kan yadda za a dinga kasha fan miliyan dayar.

A cikin wasikar sun bukaci a kawo karshen hauhawar farashin tikiti a filaye daban daban, musammam yadda ake yi idan babbar kungiya za ta kara a wasa.

'Yan kallon za suyi zanga zangar ne mako guda da mahukuntan gasar suka kulla kwantiragi da Sky da kuma BT Sports da ta kai sama da kudi fam biliyan biyar a tsawon shekaru uku da za ta fara aiki daga kakar wasa ta 2016-17.