Walcott ya karyata zargin rikici da Wenger

Theo Walcott Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Theo Walcott ya koma Arsenal a Janairun 2013

Dan kwallon Arsenal, Theo Walcott, ya karyata zargin yin sa-in-sa tsakaninsa da kocinsa Arsene Wenger, ya kuma ce bai shirya ranar da za a tattauna tsawaita kwantiraginsa ba.

Kwantiragin Walcott da Arsenal zai kare ne a karshen kakar wasan 2016, kuma Wenger ya ce yana fatan za a sabunta nan bada dadewa ba.

Walcott ya sabunta kwantiraginsa a baya da Arsenal a Janairun 2013, lokacin da ya rage saura watanni shida ya zama ba shi da kulob din da yake yi wa wasa.

Dan kwallon bai buga wa Ingila gasar kofin duniya ba, sakamakon jinyar da ya yi ta watanni 10, ya kuma buga wa Arsenal wasanni 13 a gasar bana.