Brazil ta lallasa Faransa da ci uku da daya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Brazil ta sha kunya a gasar cin kofin duniya

Brazil ta samu galaba a kan Faransa da ci uku da daya a wasan sada zumunci da suka buga.

Nasarar ita ce ta bakwai da Brazil ta samu tun bayan da Jamus ta lallasa ta a gasar cin kofin duniya a shekarar 2014.

Raphael Varane ne ya ci wa Faransa kwallon farko sai kuma Oscar da Neymar da kuma Gustavo ne suka ci wa Brazil kwallo.

Carlos Dunga ne ya maye gurbin Luiz Felipe Scolari wanda ya yi murabus bayan kamalla gasar cin kofin duniya.

Kuma har yanzu babu kasar da ta doke Brazil tun lokacin da Dunga ya soma jan ragama.