Terry ya ci gaba da murza leda a Chelsea

Hakkin mallakar hoto
Image caption Terry ya lashe kofuna 13 a Stamford Bridge

Kyaftin din Chelsea, John Terry ya tsawaita kwantaraginsa domin ci gaba da taka leda a kulob din har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Dan shekaru 34 wanda kwangilarsa za ta kare a kakar wasa ta bana, ya buga wa Chelsea wasanni 550 a gasar Premier ta Ingila.

A halin yanzu dai Chelsea na da tazarar maki shida a saman teburin gasar Premier.

Kocin kulob din Jose Mourinho ya ce "Sabuwar kwangilar nuna godiya ce ga John Terry."

Terry ya lashe kofuna 13 tare da Chelsea tun bayan da ya soma taka leda a shekarar 1998.

Daga cikin kofunan da ya lashe hadda na zakarun Turai da na Europa.