An yi wa kociyan Italiya Conte barazanar kisa

Antonio Conte
Image caption Conte ya ce Marchisio ya ji rauni ne a lokacin atisaye

An yi barazarar kashe kociyan Italiya Antonio Conte bisa raunin da dan kwallon Juventus Claudio Marchisio ya ji, in ji shugaban hukumar kwallon kafar Italiya.

An yi zargin Marchisio ya karye a gwiwarsa a lokacin da tawagar kwallon kafar ke atisayen da za ta kara da Bulgeria a wasan neman gurbin shiga gasar kofin Nahiyar Turai.

Daga baya ne kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta bayar da tabbacin cewar dan wasan bai karye ba.

Shugaban hukumar kwallon Italiya Carlo Tavecchio ya sanar a wata kafar yada labarai cewar kociyan ya samu barazarar daukan ransa a shafinsa na Internet.

Italiya ta tashi wasa 2-2 da Bulgeria a wasan neman shiga gasar kofin Nahiyar Turai a ranar Asabar, za kuma ta buga wasan sada zumunta da Ingila ranar Talata.