Brazil ta doke Chile da ci daya mai ban haushi

Brazil Chile Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne wasa na 8 da Brazil ta lashe a karkashin koci Dunga a karo na biyu da tawagar

Tawagar kwallon kafar Brazil ta doke Chile da ci daya mai ban haushi a wasan sada zumunta da suka kara ranar Lahadi a filin wasan Arsenal Emirates.

Brazail ta ci kwallonta ta hannun Danilo mai buga tamaula a kulob din Hoffenheim na Jamus saura minti 18 a tashi daga wasan.

Wannan ne wasa na takwas da kociyan Brazil Dunga ya lashe a jere tun lokacin da ya karbi ragamar jagorancin tawagar kwallon kafar kasar karo na biyu.

Kuma a ranar 1 ga watan Yuni ne Brazil za ta fitar da sunayen 'yan wasan da za su wakilce ta a Copa America da Chile za ta karbi bakunci ranar 11 ga watan Yuni.