Zaben BBC na 'yar kwallon duniya

BBC Female Footballa Award
Image caption Wannan ne karon farko da BBC ta kirkiro kyautar karrama 'yar kwallon kafa

A karon farko BBC ta kirkiro kyautar karrama 'yar wasan kwallon kafa da ta fi yin fice a duniya a bana.

Wannan dama ce da magoya baya za su zabo 'yar kwallon da ta fi taka leda a shekarar nan, domin lashe kyautar da BBC za ta bayar a karon farko da wata kafar yada labarai za ta yi.

Za a karrama duk wacce ta samu nasara a daya daga cikin manyan wasannin da ya fi bunkasa da sauri a duniya.

Kuma kwararru da suka hada da jami'ai da kociyoyi da tsoffin 'yan wasa ne za su fitar da sunayen 'yan kwallo biyar , domin fitar da wacce za ta fara lashe kyautar.

Za a bayyana sunayen 'yan wasa biyar da aka zabo ranar 26 ga watan Afirilu, sannan a fitar da wacce za ta lashe kyautar a cikin watan Mayu.