An gargadi Gasar Premier game da barasa

Kwallon Nike Ordem 2 wacce ake amfani da ita don wasannin Gasar Premier
Image caption Bankin Barclays na na daukar nauyin Gasar Premier a kan dala miliyan sittin duk shekara

Manyan kungiyoyin lafiya fiye da 40 sun gargadi hukumomin da ke kula da Gasar Premier ta Ingila game da amincewa kamfanonin barasa su rika daukar nauyin gasar.

A wata wasika da suka aikewa masu kula da gasar, kungiyoyin sun ce akwai bukatar kare lafiyar matasa.

Gasar ta Premier ce dai gasar da aka fi kalla a duniya.

Daukar nauyin gasar da Bankin Barclays—wanda yake biyan dala miliyan 60 duk shekara—ke yi na daf da karewa.

An ba da rahoton cewa akwai kamfanin barasa na Diageo a cikin kamfanonin da ke kan gaba wajen neman izinin daukar nauyin gasar.