Janza ya ce Zambia ta yaudare shi

Honour Janza Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Janza ya ce ya harzuka da abin da hukumar kwallon Zambia ta yi masa

Kociyan Zambia mai barin gado Honour Janza, ya ce hukumar kwallon kafar kasar ta yaudare shi da ta ce za ta sauya shi.

Hukumar kwallon Zambia ta sanar da shirin maye gurbin kocin ne ta kafafen yada labarai ranar Lahadi a lokacin da Janza ya jagoranci tawagar wasan sada zumunta da Rwanda.

Janza ya ce "Abin takaici babu wanda ya sanar da ni daga mahukunta sai labarin na gani a jaridu, ban ji dadin hakan ba, kuma ba zan sake amince wa kowa ba"

Zambia ta dauki Janza a matsayin kociyanta a watan Agustan 2014, bayan da Patrice Beaumelle ya ajiye aikin.

Shi ne kuma ya jagoranci kasar a gasar kofin nahiyar Afirka da aka yi a Equatorial Guinea, a inda ya kasa kai kasar wasan zagaye na biyu.