Golf : Woods ba ya cikin jerin 'yan wasa 100

Tiger Woods Hakkin mallakar hoto Press Association
Image caption Woods yanzu yana mataki na 104 a jerin 'yan wasan da suka fi iya kwallon golf a duniya

A karon farko Tiger Woods ya fice daga cikin jeren 'yan wasan kwallon golf 100 da suka fi yin fice a wasan a duniya.

Woods, wanda ya lashe manyan kyautuka sau 14, kuma ya rike matsayi na daya tsawon makwanni 683, yanzu ya dawo mataki na 104 a duniya.

Rabon kuma da dan wasan mai shekaru 39 ya buga kwallon golf tun lokacin da ya fice daga gasar Farmers Insurance Open ranar 6 ga watan Fabrairun 2014.

Haka kuma rabon da Woods ya fice daga jerin 'yan wasan kwallon golf 100 da suka fi yin fice a duniya tun a cikin watan Satumbar 1996, lokacin da yake a mataki na 225.

Kuma dan wasan ya fara dare matsayi na daya a duniya ne bayan da ya lashe gasar US Open a shekarar 1997.