An dakatar da Bardsley buga wasanni 3

England FA
Image caption Tuni Bardsley ta amince da hukuncin da aka yanke mata

Hukumar kwallon kafar Ingila ta dakatar da 'yar wasan Ingila da Manchester City Karen Bardsley daga buga wasanni uku.

Tun farko hukumar kwallon ta tuhumi 'yar wasan ne da rashin da'a da kuma tayar da yamutsi a wasan da suka kara da Birmingham a ranar Lahadi.

An nuna Bardsley da Freda Ayisi a wani faifan bidiyo lokacin da suke naushin junansu a gasar Super League da suka kara.

Barsdley ta nemi afuwar laifin da ta aikata, sannan ba za ta buga karawar da za su yi da Sunderland da Arsenal da kuma kofin kalubale wasan daf da na kusa da karshe da Birmingham ba.