Falcao ya yi kan-kan-kan a zura kwallo a Colombia

Radamel Falcao Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Falcao yana son ya ci gaba da buga kwallo a United

Dan kwallon da yake wasa aro a Manchester United Radamel Falcao ya yi kan-kan-kan a tarihin cin kwallaye a tawagar kwallon kafar Colombia.

Falcao ya ci wa Colombia kwallo a wasan sada zumunta da suka doke Kuwait da ci 3-1 kuma kwallo na 24 da ya ci, wanda Arnoldo Iguaran ya ci wa kasar tun a baya.

Dan wasan ya ci kwallaye uku ke nan a wasannin sada zumunta da suke yi a Gabas ta tsakiya, wanda ya fara zura biyu a ragar Bahrain a wasan farko da suka lashe da ci 6-0.

Falcao -- mai shekaru 29 -- ya zura kwallaye hudu daga cikin wasanni 22 da ya bugawa Manchester United a bana.

Colombia tana buga wasannin sada zumunta ne domin tunkarar gasar Copa America da za a yi a Chile a cikin watan Yuni.