Kofin duniya na mata: Za a yi amfani da na'ura

Women World cup Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karon farko da FIFA za ta yi amfani da na'urar a gasar wasan kwallon kafar mata

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta sanar da cewar za ta yi amfani da na'urar da za ta sanar da alkalin wasa idan kwallo ya shiga raga.

Wannan ne karon farko da hukumar za ta yi amfani da na'ura a daya daga cikin manyan wasannin kwallon kafar mata a duniya.

Na'urar tana amfani da kyamara guda takwas a raga da take tantance idan kwallo ta shiga raga domin sanar da alkalin wasa.

Kuma a cikin dakika daya take ankarar da alkalan wasa idan kwallo ta shiga raga ko kuma ba ta shi ga ba.

Za a fara gasar cin kofin duniyar ta mata ranar 6 ga watan Yuni zuwa 5 ga watan Yuli da za a yi a filayen wasa da suka hada da na Edmonton da Moncton da Montreal da Ottawa da Vancouver da kuma filin Winnipeg.