Yarima Ali ya nemi goyon bayan CAF

Prince Ali Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a yi zaben shugabancin FIFA a cikin watan Mayu

Dan takarar kujerar shugabancin FIFA Yerima Ali Bin Al Hussein ya ce yana fatan zai samu goyon baya daga Afirka bisa takarar da yake yi.

Yarima Ali, mai shekaru 39, mataimakin shugaban FIFA yana daga cikin 'yan takara uku da suke zawarcin shugabancin kujerar FIFA tare da Blatter.

Nahiyar Afirka tana da kuri'u 54 daga cikin 209 da mambobin kasashe FIFA za su kada a zaben shugabanta a ranar 29 a watan Mayu a Zurich.

Mako mai zuwa Yarima Ali zai ziyarci babban taron hukumar kwallon kafar Afirka a Alkahira tare da sauran 'yan takara Michael van Praag da kuma Luis Figo.

Shugaban FIFA Sepp Blatter wanda ya fara jagorantar FIFA tun daga shekarar 1998 yana fatan a sake zabensa karo na biyar a jere.