Wenger da Giroud sun samu lambar yabo

Image caption Arsene Wenger da Giroud sun samu lambar yabo ta Barclays

Kociyan kulob din Arsenal, Arsene Wenger, ya lashe lambar yabo na Barclays na kociyan da ya fi kowa a wata, yayin da dan wasan gaba Olivier Giroud kuma ya karbi lambar zakakan dan wasa.

kulob din Arsenal ya yi nasara sau hudu a jere a wasannin gasar Premier a watan Maris, inda ya ci kwallaye tara, shi kuma aka zura masa kwallaye biyu a raga.

Dan wasan kasar Faransa, Giroud ya zura kwallaye biyar a raga, inda yaci kulob din Everton da QPR da kuma West Ham.

Arsenal ce ta uku a teburin gasar Premier, inda ta ke da sauran wasanni takwas da zata buga. Chelsea dai na gaban Arsenal da maki bakwai ne.

Arsenal za ta karbi bakuncin Livepool a wasan da zasu buga ranar Asabar a filin wasa na Emirates.

Wasannin da su ka rage wa Arsenal sun hada da karawar da zasu yi da Chealsea ranar 26 ga watan Aprilu da kuma wanda za su yi da Manchester a ranar 17 ga watan Mayu.