Caf za ta zabi wakilan Africa a FIFA

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana sa ran yi wa tsarin mulkin CAF gyara domin Hayatou ya ci gaba da shugabanci

Hukumar kula da kwallon kafar Africa (CAF) za ta zabi mutane biyu wadanda za su wakilci nahiyar a hukumar kwallon kafar duniya.

Ana sa ran hukumar ta CAF za ta zabi dan kasar Tunisia, Tarek Bouchamaoui da takwaran aikinsa na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Constant Omari Selemani, ranar Talata, domin wakiltar nahiyar a hukumar ta FIFA, mai mambobi 25.

Ana sa ran mutanen biyu za su kayar da dan kasar Ivory Coast, Jacques Anouma, wanda ya shafe shekaru takwas a kan mukamin.

Wakilai daga kasashe 54 da za su yi zaben sun bukaci a soke batun yawan shekaru daga tsarin mulkin hukumar domin bai wa shugabanta Issa Hayatou damar ci gaba da shugabanci idan wa'adinsa ya kare.

Dokar CAF dai ta bukaci duk wani jami'inta da ya kai shekaru 70 a duniya ya sauka daga mukaminsa, sai dai ana sa ran za a yi garanbawul a kudin tsarin mulkinta domin kawar da wannan doka.