Liverpool: Rodgers ya kare 'yan wasansa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Brendan Rodgers ya ce yana sa rai za su kai-labari

Kociyan Liverpool, Brendan Rodgers, ya kare 'yan wasansa, yana mai cewa suna da kwazo da jajircewa bayan Arsenal ta doke su da ci 4-1 ranar Asabar.

Wannan shan kashi da suka yi -- wanda shi ne na biyu a jere -- ya sa kulob din ya yi asarar maki bakwai a gasar cin Kofin Zakarun Turai.

Lamarin dai ya sa sai da 'yan Liverpool suka yi taro, wanda a cikinsa aka yi ta zargin juna a kan dalilinsu na shan kashi.

Sai dai Rodgers ya ce: "Kulob din yana fuskantar kalubale, amma duk da haka ba ma shakkar kwazo da jajircewarmu. Wannan a bayyane yake."

Ya kara da cewa: "Muna gudanar da taruka da dama inda muke yin bitar irin rawar da muka taka a dukkanin wasannin da muka yi. Don haka wannan taron ba shi da bambanci da wadancan."

Kociyan na Liverpool ya ce bai fitar da rai ba da kasancewa a cikin kulob hudu da za su zamo kan gaba a teburin Gasar, duk da kashin da suka sha a wasansu na ranar Asabar.