Caf ta zabi mambobin kwamitin Fifa

Blatter Hayatou Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mambobin za su wakilci Afirka shekaru biyu a kwamitin amintattun Fifa

Hukumar kwallon kafar Afirka ta zabi Tarek Bouchamaoui da Constant Omari Selemani a matsayin mambobinta a kwamitin amintattu na Fifa.

Bouchamaoui dan Tunisia ya lashe zaben ne ba tare da hamayya ba, a yayin da Omari daga Jamhuriyar Congo ya doke Jacques Anouma daga Ivory Coast.

Tun a farko Mohamed Raouraoua daga Algeria fice wa ya yi daga takarar tun kafin a fara kada kuri'u.

Mambobin da aka zaba za su wakilci hukumar kwallon kafar Afirka tsawon shekaru biyu a cikin kwamitin amintattun Fifa.

A lokacin, shugaban Caf Issa Hayatou ya ce nahiyar Afirka za ta goyi bayan takarar Sepp Blatter a matsayin shugaban Fifa a watan gobe.