Watakila a sayar da Crystal Palace

Image caption Ana ci gaba da tattaunawa da masu sha'awar mallakar kulob din Crystal Palace

Daya daga cikin mutanen da suka mallaki kulob din Crystal Palace, Steve Parish, ya ce babu wani shiri a kasa a kan sayar da kulob din, amma ana ci gaba da tattaunawa da masu sha'awar mallakarsa.

A bara ne dai aka yi hasashen babban mai arzikin nan dan Amurka Josh Harris, zai sayi kulob din.

Mr Parish ya ce suna bukatar karin zuba jari ne kawai domin su inganta filin wasan kwallo na Selhurst Park.

A cewarsa, "Dalilin mu na neman kudi shi ne domin mu kara inganta kayayyakin more rayuwa. Ba wani abin gaggawa, kuma muna kan tsarin da ya dace. Idan zai yiwu to zai yiwu kawai."

Ya kara da cewa tuntuni ya kamata a yi gyare-gyaren amma an kasa saboda yawan kudin da za a kashe.

"Idan hakan na nufin mu shigo da wasu mutane cikin al'amarin kuma muka tabbatar sun cancanta, to za mu yi haka din," in ji Mr Parish

Parish dai yana daya daga cikin mamallakan kulob din Palace tun shekara ta 2010 lokacin da aka yi yarjejeniyar ceto kulob din daga durkushewa.