Liverpool za ta ziyarci Blackburn a kofin FA

Blackburn Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool tana mataki na biyar a teburin Premier da maki 54

Liverpool za ta ziyarci Blackburn a gasar cin kofin kalubale wasa na biyu na daf da na kusa da karshe a ranar Laraba.

Tuni Liverpool din ta sanar da cewar 'yan wasanta uku da suka hada da Steven Gerrard da Martin Skrtel da kuma Emre Can ba za su buga a karawar ba.

Haka kuma Liverpool din tana duba yiwuwar idan Balotelli zai iya buga mata wasan, ganin bai buga karawar da suka yi da Arsenal a gasar Premier ranar Asabar ba.

Wasan farko da suka kara da Blackburn a kofin kalubale a Anfield, tashi suka yi babu ci.