2017: Gabon ce za ta karbi bakuncin kofin Afirka

Afcon 2017 Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karo na biyu da Gabon za ta karbi bakuncin gasar kofin nahiyar Afirka.

Hukumar kwallon kafar Afirka Caf ta zabi kasar Gabon a matsayin wacce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2017.

Kwamitin zartarwa ne ya zabi Gabon wacce ta yi takarar karbar bakuncin gasar tare da Algeria da Ghana.

Wannan ne karo na biyu da kasar za ta karbi bakuncin gasar, bayan da ta dauki bakuncin hadin gwiwar wasannin a shekara ta 2012 tare da Equatorial Guinea.

Tun farko kasar Libya ce yakamata ta karbi bakuncin kofin Afirkan, amma sakamakon yakin basasa da ake yi a kasar yasa ta janye daga karbar bakuncin gasar.

Caf din dai za ta fitar da jaddawalin kasashen da za su buga wasannin neman gurbin shiga gasar ta 2017 ciki har da Morocco da Tunisia ranar Laraba.