Nigeria ta yi kasa a jerin Fifa

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Nigeria ta koma mataki na 8 a Afirka a jerin kasashen da suka fi iya taka leda

Tawagar Super Eagles ta Nigeria ta yi kasa a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Afirka da Fifa ta fitar na watan Afirilu.

Nigeria ta koma mataki na takwas a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Afirka kuma ta 42 a jerin da Fifa ta fitar.

A watan Maris da ya gabata Nigeria tana matsayi na bakwai a Afirka kuma ta 41 a duniya a jerin kasashen da suka fi yin fice.

Kasar Algeria dai ta ci gaba da zama a mataki ta daya a nahiyar Afrika kuma ta 21 a jerin kasashen da Fifa ta fitar a watan na Afirilun.

Ivory Coast wacce ta dauki kofin nahiyar Afirka a bana tana matsayi na biyu a Afirka kuma mataki na 23 a duniya.

Ga Jerin kasashe 10 da Fifa ta fitar na watan Afirilu a nahiyar Afrika.

1. Algeria 2. Côte d'Ivoire 3. Ghana 4. Tunisia 5. Senegal 6. Cape Verde 7. Guinea 8. Nigeria 9. Kamaru 10. Congo