Kyautar Ballon d'Or tana da nakasu a tamaula

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho ya ce ya goyi bayan Wenger cewar Ballon d'Or tana kawo nakasu ga kwallon kafa

Kociyan Chelsea Jose Mourinho ya ce kyautar da ake bai wa dan kwallon kafar da ya fi yin fice a duniya wato Ballon d'Or tana kawo nakasu ga wasan kwallon kafa.

Kocin ya ce ya goyi da bayan mai horar da Arsenal Arsene Wenger wanda ya ce an fi fifita dan kwallo mai makon kungiyar da yake yin wasa.

Mourinho ya ce "Kwallon kafa ta fara barin muradin da aka santa da shi na yaba wa kwazon kulob an karkata zuwa fifita dan wasa guda".

Mourinho wanda ya lashe gasar kofuna bakwai a kasashe hudu da kuma kofin Zakarun Turai ya ce kwallon kafa kwazon 'yan wasan kulob ne ba dan wasa daya ba.

Cristiano Ronaldo na Real Madrid ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi yin fice a duniya a bana karo na uku kuma da ya lashe kyautar kenan.