Liverpool ta dinke baraka — Rodgers

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto s
Image caption Liverpool tana mataki na biyar a teburin Premier da maki 54

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce taron da ya yi da 'yan wasa kan doke su da aka yi a wasanni ya taimaka musu samun galaba kan Blackburn a kofin FA.

Liverpool ta yi taron ne bisa doke su da Manchester United da Arsenal suka yi a jere a gasar Premier.

Kuma kulob din ya gudanar da taron ne bayan da ya dinga samun suka daga magoya baya kan yadda abokan hamayya suka doke su a karawar da suka yi.

Rodgers ya ce "Taron da suka yi bai banbanta da wanda suke yi a baya ba, illa wannan karon sun hadu da kalubale ta bangare da dama".

Liverpool ta kai wasan daf da karshe a kofin kalubale bayan da suka doke Blackburn da ci daya mai ban haushi a Ewood Park ranar Laraba.