Na samu nasarori a Tottenham — Sherwood

Tim Sherwood Hakkin mallakar hoto z
Image caption Aston Villa tana mataki na 16 a teburin Premier da maki 29

Kocin Aston Villa Tim Sherwood ya ce ya samu nasarori da dama a lokacin da ya horar da kulob din Tottenham.

Sherwood wanda kulob dinsa Aston Villa zai kara da Tottenham a gasar Premier ranar Asabar, an sallame shi a White Hart Lane kwanaki biyu bayan da ya jagoranci kulob din karewa a matsayi na 6 a teburin Premier.

Kocin ya karbi ragamar jagoranci Spurs a watan Disambar 2013, kuma ya samu nasarorin da babu wani kociya da ya samu a kulob din.

Wanda ya gaje shi Mauricio Pochettino ya dauko karin 'yan wasa biyar, amma har yanzu kulob din yana matakin da ya kare a lokacin da aka kori Sherwood.