An haramtawa Ibrahimovic buga wasanni hudu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zlatan Ibrahimovic ya yi zage-zage

An dakatar da dan wasan Paris St-Germain, Zlatan Ibrahimovic, daga buga wasannin Ligue 1 guda hudu bayan ya yi zagi a wasan da suka yi da kulob din Bordeaux a Faransa.

Dan wasan dan kasar Sweden ya fusata ne, sannan ya soki alkalan wasa bayan kulob dinsa ya sha kashi a hannun Bordeaux da ci 3-2 a fafatawar da suka yi a watan jiya.

Ibrahimovic, mai shekaru 33, ya bayar da hakuri daga baya, yana mai cewa bai yi kalaman domin ya bata sunan Faransa ko 'yan kasar ba.

Yanzu dai an haramta masa buga wasanni hudu a cikin bakwai da kulob dinsa zai yi.

Wani kwamitin da'a ya ce ya dauki matakin ne saboda "kalaman batanci da mummunar halayar" da dan wasan ya nuna.

Kazalika an haramtawa Ibrahimovic buga wasan farko da kulob dinsa zai yi da Barcelona a matakin dab da na kusa da karshe a gasar cin Kofin Zakarun Turai .

Amma zai iya buga wasan karshe na gasar cin kofin League da za su fafata da Bastia.