Sherwood ya kwashi maki uku a Tottenham

Christian_Benteke Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Aston Villa ta koma matsayi na 15 a teburin Premier

Aston Villa ta doke Tottenham da ci daya mai ban haushi a White Hart Lane a gasar Premier da suka kara ranar Asabar.

Christian Benteke ne ya ci kwallon da ta bai wa Aston Villa maki uku saura minti 10 a ta fi hutu, kuma nasarar farko da Sherwood ya samu tun bayan da Tottenham ta sallame shi.

Villa ta karasa karawar da 'yan wasa 10, bayan da aka bai wa Carlos Sanchez jan kati daf da za a tashi daga wasan.

Da wannan nasarar Aston Villa ta koma mataki na 15 a teburin Premier da maki 32.

Ga sakamakon wasu wasannin da aka buga ranar Asabar:

Swansea 1 - 1 Everton Southampton 2 - 0 Hull Sunderland 1 - 4 Crystal Palace Tottenham 0 - 1 Aston Villa West Brom 2 - 3 Leicester West Ham 1 - 1 Stoke