Man United ta samu kwarin gwiwa — Kompany

Van Persie Kompany
Image caption United tana matsayi na uku a teburin Premier da maki 62, City tana da maki 61 a mataki na hudu

Kyaftin din Manchester City Vincent Kompany ya ce Manchester United tana da kwarin gwiwar da za ta iya lashe wasan hamayya da za su kara.

Manchester City wacce ta lashe wasanni biyar baya da suka kara a jere za ta ziyarci filin wasa na Old Trafford ranar Lahadi a gasar Premier wasan mako na 32.

Kompany mai shekaru 29 ya ce "United tana matukar son lashe wasan, domin mun dade muna doke su a haduwar da muka dinga yi".

United ta doke Aston Villa da ci 3-1 a ranar Asabar a Old Trafford, yayin da Manchester City ta yi rashin nasara a gidan Crystal Palace da ci 2-1.