Okocha ya bukaci NFF ta kawar da takaddamar koci

Jay Jay Okocha Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Okocha ya ce ya kamata NFF ta kawar da takaddama kan daukar kocin Super Eagles

Tsohon dan wasan Nigera Jay-Jay Okocha ya yi kira ga hukumar kwallon kafar Nigeria wato NFF ta kawar da takaddamar aikin horar da Super Eagles.

Okocha ya ce ya yi kiran ne domin a mangance koma bayan da tawagar kwallon kafar Nigeria ke shiga game da batun daukar koci.

Daniel Amokachi ne ya jagoranci Super Eagles tun daga watan Disamba, bayan da aka dauki lokaci mai tsawo ana tattaunawa kan batun sabunta kwantiragin Steven Keshi.

Kuma makwonni biyu da suka wuce ne Amanju Pinnicks ya sanar da bai wa Keshi kwantiragin shekaru biyu ya horar da Nigeria amma har yanzu ba su rattaba hannu ba.

Okocha ya bukaci a kawo karshen siyasar daukar koci a Nigeria domin a kauce wa kara rashin halartar gasar kofin nahiyar Afirka na gaba.