Bale yana da muhimmaci a Madrid — Ancelotti

Ancelott Bale Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Madrid za ta ziyarci Atletico ranar Talata a wasan daf da na kusa da karshe

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce Gareth Bale yana da rawar da zai taka a kokarin da suke na lashe kofin zakarun Turai na bana.

Madrid wacce ita ke rike da kofin bara, za ta kara a wasan hamayya da Atletico Madrid a wasan daf da na kusa da karshe ranar Talata.

Bale, wanda yana daga cikin 'yan wasan da suka ci wa Madrid kwallo a wasan karshe a bara, yana shan suka kan kasa taka rawar gani a bana.

Ancelotti ya ce yana fatan dan kwallon zai murmure kafin wasan domin yana da rawar da zai taka a karawar.

Bale, wanda ya koma Madrid a watan Satumbar 2013 bai buga wasan da Madrid ta doke Eibar 3-0 a La Liga ba sakamakon jinya da ya yi.