Maurinho bai yi tir da halayar magoya bayan QPR ba

Cesc Fabregas Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na daya a teburin Premier za kuma ta karbi bakuncin United ranar Asbar

Kociyan Chelsea Jose Mourinho ya ki ya yi tir da magoya bayan QPR bisa jifan da suka yi a filin wasa a karawar da suka yi ranar Lahadi.

Magoya QPR din sun yi ta jifa a cikin filin a lokacin da Cesc Fabregas ya zura musu kwallo a raga a Loftus Road.

Jefe jefen da suka yi sun sa sai da kwalbar roba ta doki kan Branislav Ivanovic lokacin da suke yin murnar kwallon da suka ci.

Mourinho ya ce an yi wasa lafiya, an kuma tashi lafiya kuma shi bai ga lokacin da aka yi jifa a cikin filin ba.

Chelsea ta ci gaba da zama a mataki na daya a teburin Premier da maki 73, kuma za ta karbi bakuncin Manchester United ranar 18 ga wannan watan.