Tikitin wasan Arsenal da Chelsea ya kai naira dubu 278

Arsenal Team Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal za ta kara da Chelsea a wasan mako na 33 a gasar Premier

Ana sayar da tikiti daya na kallon karawar da Arsenal za ta karbi bakuncin Chelsea a gasar Premier a Emirates a intanet a kan fam 950, kwatankwacin naira 278,350.

Tun farko an gama sayar da tikitin karawar da kungiyoyin za su fafata ranar 26 ga watan Afirilu, amma an ci gaba da hadahadar sayar da tikitin a Intanet.

Kudin kallon wasan hamayya a filin Emirates musamma fafatawa da Chelsea ya kan kai fam 95, kwatankwacin naira 27,835 a karamin bene.

Kudin tikitin kallon wasannin Arsenal a Emirates shi ne mafi tsada a gasar Premier.

Arsenal tana matsayi na biyu a teburin Premier, a inda Chelsea wacce take mataki na daya ta ba ta tazarar maki bakwai a teburin.