Atletico da Madrid sun tashi wasa canjaras

Iker Casillas
Image caption Za su buga wasa na biyu ranar 22 ga watan Afirilu

Atletico Madrid da Real Madrid sun tashi canjaras a wasan hamayya da suka buga a gasar cin kofin zakarun Turai a filin wasa na Vicente Calderon ranar Talata.

Sai dai mai tsaron ragar Madrid Iker Casillas ya kafa tarihin wanda ya fi yawan buga gasar, a inda ya buga wasannin 147, Xabi na Barcelona ya buga wasanni 146.

A Italiya kuwa kungiyar Juventus ce ta doke Monaco da ci daya mai ban haushi, a inda Vidal ya zura kwallon a minti na 11 da dawo wa daga hutu.

Za kuma a buga wasa na biyu ne a ranar 22 ga watan Afirilu.