Messi ya sha fama da jinya a kakar bara

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona za ta kara da PSG a gasar kofin zakarun Turai ranar Laraba

Dan kwallon Barcelona Lionel Messi ya ce bai ji dadin buga wasanni a kakar wasan bara ba, bisa yadda ya yi ta yi jinya a karo da dama.

Messi ya kara da cewar ya yi takaici a baran kan rashin buga wasanni da dama, amma yanzu ya dawo kan ganiyarsa.

Sai dai kuma a kakar wasan bana dan kwallon ya ci kwallaye 45 a raga daga cikin wasanni 44 da ya buga.

Dan wasan dan kasar Argentina bai dauki kofi a Barcelona a bara ba, kuma Jamus ta doke su a wasan karshe a kofin duniya a Brazil a shekarar 2014.

Barcelona za ta kara da Paris St-Germain a wasan farko na cin kofin zakarun Turai ranar Laraba a Camp Nou.

Messi mai shekaru 27 saura kwallo daya ya cike ta 400 da ya ci wa Barcelona wacce za ta fuskanci PSG karo na uku a bana.