Barcelona ta doke PSG da ci 3-1 a Faransa

Luis Suarez Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Za su buga wasa na biyu ranar 21 ga watan Afirilun nan

PSG ta yi rashin nasara a hannun Barcelona da ci 3-1 a gasar cin kofin zakarun Turai da suka kara a Faransa ranar Laraba.

Neymar ne ya fara zura kwallo a raga kafin Luis Suarez ya kara kwallaye biyu bayan da aka dawo daga hutu.

PSG ta rage kwallo guda ta hannun Gregory van der Wiel, bayan da Mathieu ya ci kansu saura minti takwas a tashi daga karawar.

Itama FC Porto doke Bayern Munich ta yi da ci 3-1 a fafatawar da suka yi a Portugal.

Quaresma ne ya ci kwallaye biyu, Bayern ta farke kwallo daya ta hannun Thiago Alcántara kuma Porto ta kara ta uku ta hannun Martínez.

Za su fafata a wasan karo na biyu ranar 21 ga watan Afirilu.