Magoya bayan Newcastle na shirin kaurace wa wasa

Newcastle United Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Newcastle ta yi rashin nasara a hannun Liverpool da ci 2-0 a gasar Premier ranar Litinin

Magoya bayan kulob din Newcastle suna shirin kaurace wa kallon wasan da zai buga da Tottenham a gasar Premier ranar Lahadi.

Newcastle yana da kudin ajiya a banki da ya kai fam miliyan 34, kuma tun a baya ya bayar da sanarwar cin ribar sama fa fam miliyan 18 a kakar wasan 2013-14.

Magoya bayan Newcastle suna kalubalantar mai kulob din Mike Ashley kan yadda yake gudanar da kulob din.

Haka kuma sun zarge shi da kin sayo zaratan 'yan wasa da za su kai ga kungiyar samun nasarori a wasannin da take buga wa.

Newcastle tana matsayi na 13 a teburin Premier da maki 35, kuma za ta karbi bakuncin Tottenham wadda take mataki na bakwai da maki 57.