Kofin Zakaru: PSG za ta karbi bakuncin Barcelona

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karo na takwas da kungiyoyin biyu za su kara

Kungiyar Paris St-Germain za ta karbi bakuncin Barcelona a gasar cin kofin zakarun Turai wasan daf da na kusa da karshe ranar Laraba.

PSG ta Faransa wacce ba ta taba daukar kofin zakarun Turan ba, tana fatan ta doke Barcelona wacce ta lashe kofin sau hudu a tarihin gasar.

Wannan kuma shi ne karo na takwas da kungiyoyin za su fafata a wasannin cin kofin zakarun Turai.

Dukkansu kungiyoyin sun sami nasara a wasanni biyu sannan suka buga canjaras a wasannin uku da suka buga a baya.

A wasannin bara PSG ce ta doke Barcelona da ci 3-0 a Faransa, wasa na biyu Barca ce ta samu nasara da ci 3-1 a Spaniya.

Ga tarihin wasannin da kungiyoyin suka kara a tsakaninsu:

2014/2015

  • Kofin zakaru Barcelona 3 - 1 Paris St-G.
  • Kofin zakaru Paris St-G. 3 - 2 Barcelona

2012/2013

  • Kofin zakaru Barcelona 1 - 1 Paris St-G.
  • Kofin zakaru Paris St-G. 2 - 2 Barcelona

1996/1997

  • Kofin Euro Cup Barcelona 1 - 0 Paris St-G.

1994/1995

  • Kofin zakaru Paris St-G. 2 - 1 Barcelona
  • Kofin zakaru Barcelona 1 - 1 Paris St-G.