Walcott zai ci gaba da wasa a Arsenal — Wenger

Theo Walcott Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wenger yana fatan Walcott ya buga karawar da za suyi da Reading a kofin FA

Koci Arsene Wenger ya ce yana da tabbacin cewar Theo Walcott zai ci gaba da taka leda a kungiyar Arsenal.

Sauran shekara daya kwantiragin Walcott da Arsenal ta kare, kuma ana rade-radin zai koma wasa Liverpool a karshen kakar bana.

Dan wasan wanda ya zura kwallaye 77 a raga daga wasanni 203 da ya buga wa Arsenal, bai buga wasanni biyar ba a jere sakamakon jinyar raunin da ya ji a gwiwarsa.

Haka Wenger ya ce yana fatan Mikel Arteta da kuma Tomas Rosicky za su amince su sabunta kwantiraginsu.