"Sau biyu na buga kwallo ta tsakanin kafafun Luiz"

Luis Suarez David Luiz Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ranar 21 ga watan Afirilu Barca za ta karbi bakuncin PSG a wasa na biyu a Camp Nou

Luis Suarez ya ce sau biyu yana zura kwallo ta tsakanin kafafun David Luiz a karawar da ya zura kwallaye biyu a ragar Paris St-Germain a Faransa ranar Laraba.

Cikin sauki Suarez ya zura kwallon ta tsakanin kafafun Luiz ya kuma ci wa Barcelona kwallo ta biyu ya kuma kara yin hakan ya ci ta uku a wasan.

Barcelona ce ta doke PSG a gasar cin kofin zakarun Turai wasan daf da na kusa da karshe da suka buga a Faransa.

Suarez ya ci kwallaye 17 tun lokacin da ya koma kulob din a bana, ciki har da kwallaye biyun da ya zura a ragar PSG a gasar cin kofin Zakarun Turan.

Kwallaye 31 Suarez ya ci a gasar Premier a bara a Liverpool kafin Barcelona ta dauke shi kan kudi fam miliyan 75.