Bama yin katabus a manyan wasanni — Rodgers

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An cire Liverpool daga kofin zakarun Turai da kofin FA tana mataki na biyar a teburin Premier

Kociyan Liverpool Brendan Rodgers ya ce ya kamata su kara azama idan suna buga wasa da fitattun kungiyoyi.

Kocin ya fadi haka ne bayan da Aston Villa ta fitar da su daga gasar cin kofin kalubalen Ingila a wasan daf da karshe da ci 2-1 ranar Lahadi a Wembley.

Rodgers ya ce "Wani lokacin 'yan wasan suna dari-dari da salon taka ledar, sannan sukan saka kaguwa sai sun lashe wasa, kuma shi ne yake tsaya musu a cikin zuci"

Liverpool ce ta kare a mataki na biyu a teburin Premier bara, amma a bana tana matsayi na biyar da maki 57.

Haka kuma an fitar da ita daga gasar cin kofin zakarun Turai, sannan ba ta cikin hudun farko a teburin Premier bana, kuma an cire ta a gasar FA.