Aston Villa ta kai wasan karshe a kofin FA

Aston Villa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Aston Villa ta dauki kofin kalubale na Ingila wato FA sau hudu

Aston Villa ta kai wasan karshe a kofin kalubale na Ingila, bayan da ta doke Liverpool da ci 2-1 a Wembley ranar Lahadi.

Liverpool ce ta fara zura kwallo a raga ta hannun Coutinho, sai dai kuma minti biyar tsakani Benteke ya farke kwallon yayin da daga baya Delph ya ci Liverpool kwallo ta biyu a minti na 11 da dawowa daga hutu.

Wannan ne karon farko da Villa ta kai wasan karshe a gasar FA, tun lokacin da Chelsea ta doke ta a wasan karshe a kofin a shekarar 2000.

Da wannan nasarar Aston Villa za ta kara da Arsenal ranar 30 ga watan Mayu a filin wasa na Wembley.