Tuchel zai maye gurbin Klopp a Dortmund

Tuchel Klopp Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Borussia Dortmund tana mataki na tara a teburin Bundesliga da maki 36

Tsohon kocin FSV Mainz 05 Thomas Tuchel ne zai maye gurbin Jurgen Klopp a kungiyar Borussia Dortmund daga ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa.

Tuchel wanda ya bar kulob din Mainz a bara don radin kansa, ya rattaba kwantiragin shekaru uku da Borussia Dortmund.

Tun farko an yi rade-radin cewar zai koma horar da Hamburg ne a farkon kakar bana, amma kuma kulob din ya dauki Bruno Labbadia.

Ranar Laraba ne Klopp, mai shekaru 47 ya sanar da cewar zai bar Dortmund a karshen kakar bana, bayan da ya kasa taka rawar gani a shekarar nan.

Tuni ake jita-jitar zai koma horar da kwallon kafa a Premier da Manchester United kafin ta dauko Louis van Gaal ko kuma Arsenal, sai kuma kwanan nan da ake cewa zai koma Manchester City ne.